Fintopio Update
💎 An kammala fasa dutse, ko duk wani game da ake bugawa acikin Fintopio. HP ɗin da aka tara kuma sunce za'a musanya shi zuwa coin ɗinsu mai suna HOLD anan gaba, sannan bada jimawa ba za'a iya a fara amfani dashi a matsayin 'cashback' domin biyan fee dashi acikin wallet ɗin su.
💎 Kasancewar Fintopio wallet ce, kuma Fintech, yanzu samun points ɗin su don samun airdrop zai yiwu ne kaɗai ta hanyar amfani da wallet ɗin, misali kamar wajen swapping, trading, da sauran su.
💎Duk dutse da mutun ya fasa, wanda muke gani a Inventory, zasu buɗe 'Store' ɗinsu a gaba wanda zasu ke saida kayayyaki kamar riguna, waya, hula, da sauran su, idan ka siya za'a aiko maka har inda kake, idan kuma ƙasar da kake tayi nisa, ko akwai wahalar transportation, zasu musanya maka abinda ka siya da darajarsa a USDT.
💎 Sunce suna tafe da hanyar tura crypto ta WhatsApp username, Discord username, Facebook username nan kusa In shaa Allahu. Already dama mun san sun jima da zuwa da tsarin turawa ta Teleg.ram Username, yanzu sun cimma na X ma. Haka zalika sun cimma multi chain swap. Suna building sosai da sosia wanda yake alamta mana akwai haske a gaba da alkhairi da za'a samu In shaa Allahu.
💎 Sun gyara graphics na wallet ɗinsu da Logo ɗinsu ya ƙara kyau.
____
💎 Idan kana amfani da TON Blockchain sosai, yana da kyau kake amfani da wallet ɗinsu, zasu kalli hakan sosai wajen bada airdrop da zasuyi anan gaba.
Ubangiji Allah ya bamu sa'a.